Dan ta’addan nan da ya yi kisan gilla a masallacin New Zealand, ya daukaka kara kan hukuncin daurin rai da ran da aka yanke masa.
A shekarar 2019 mutumin ya halaka musulmi 51 a daidai lokacin da suke ibada a wasu masallatai biyu da ke birnin Christchurch na kasar.
- Kasafin 2023: El-Rufa’i ya ware wa matasa masu yi wa kasa hidima a Kaduna N300m
- Kotu ta yanke wa dan siyasar China hukuncin kisa saboda karbar cin hanci
Yanzu dai makashin ya ce bai gamsu da hukuncin da kotu ta yanke masa ba, don haka ya daukaka kara.
Wata majiya daga Kotun Daukaka Karar da ke birnin Wellington, ta fada a ranar Talata cewa ba a kai ga tsayar da ranar da za a soma sauraron karar da makashin ya daukaka ba.
A watan Agustan 2020, kotu ta yanke wa Brenton Tarrant hukuncin daurin rai da rai ba tare da neman afuwa ba bayan ta kama shi da laifin kashe mutum 51 da kuma yunkurin kashe wasu 40.
Bayanai sun ce wannan hari, shi ne irinsa mafi munin da ya taba aukuwa a tarihin kasar ta New Zealand.
Munin laifin da Brenton Tarrant ya aikata, ya sa Alkalin da ya yanke masa hukunci cewa, zai tsananta sharudda a kan hukuncin ta yadda har mai laifin ya mutu ba zai iya kubuta ba.