Akalla mutane 11 ne suka mutu yayin da 6,400 suka bata a sanadin mahaukaciyar guguwar Cyclone Gabrielle a yankin Kudancin New Zealand.
Tun ranar 12 ga watan da muke ciki na Fabrairu ne guguwar ta afka wa kasar, lamarin da ya haddasa ambaliyar ruwa mai muni.
- APC ta bukaci Buhari ya mutunta umarnin Kotun Koli kan wa’adin tsofaffin kudi
- Ba mu kai samame gidan Tinubu ba —EFCC
Firaiministan kasar, Chris Hipkings ya kwatanta guguwar a matsayin babban bala’i mafi muni da kasar ta gani a wannan karni.
A cewarsa, akwai yiwuwar samun karin mutanen da suka mutu, la’akari da yawan mutanen da suka yi batan dabo sanadin guguwar.
Chris Hipkins ya ce guguwar ta shafi rayukan al’umma kai tsaye, yayin da har yanzu ta ki batar da damar da za a fara aikin ceto da lalubo wadanda suka bata
Ya bayyana takaici kan yadda guguwar ta lalata hanyoyin sadarwa, turakun wutar lantarki, da gurbata ruwan sha tare da lalata hanyoyi, yayin da ambaliyar ruwa ta shafe wasu yankunan.