’Yan sanda a kasar New Zealand sun ce sun gano asalin wasu kananan yara da aka tsinci gawarwakinsu a yashe a cikin jaka.
Hukumomin kasar sun sanar a safiyar Juma’a cewa ba za su fitar da bayanan yaran ba, kuma suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwarsu.
- Ambaliya ta kashe mutum 182 a Afghanistan
- Alkali zai biya wa saurayi sadakin N100,000 bayan iyayenta sun maka shi a kotu
Makonni biyu da suka gabata ne da hukumomin kasar suka tsinci gawarwakin yaran a wasu jaka a cikin kayan da wasu iyalai.
Iyalan sun sayi kayan makare da wata tirela ne bayan yi gwanjonsu sakamakon watsi da su da masu kayan suka a yi a Auckland, birni mafi girma a kasar.
’Yan sanda sun bayyana cewa iyalan da suka sayi kayan da aka yi gwanjon su ba su da alaka da mutuwar yaran.
Sun bayyana cewa shekarun yaran da aka gano gawarwakinsu ba su wuci ’yan makarantar firamare ba.
Dan sanda mai bincike Insfekta Tofilau Faamanuia Vaaelua ya ce mai binciken gawa ya samu izinin gudanar da bincike domin gabatar wa jama’a hujjojin da ke iya bayyana asalin yaran.
A ranar Litinin ’yan sanda a birin Seoul, babban birnin kasar Koriya ta Kudu sun ce sun gano wata mata da suke kyautata zaton tana da dangantaka da yaran.
Sun bayyana cewa a shekarar 2018 ne matar ta isa kasar, kuma tun daga lokacin ba ta sake barin kasar ba.