Fira Ministan Birtaniya, Boris Johnson, ya ba da hakuri kan karya dokar COVID-19 da kuma halartar wani bikin casun da fadarsa ta shirya a wani lambun shakatawa.
Boris Johnson ya bayar da hakurin ne bayan ya amsa cewa ya halarci taron, wanda ya ja masa caccaka da kira-kirayen neman ya sauka daga mukaminsa.
- Abin da ya sa mahauta suka daina tallar nama
- Tattalin arzikin duniya zai fuskanci koma-baya a 2022 – Bankin Duniya
Tun a shekarar 2020 Boris Johnson ya fuskantar matsin lamba daga jam’iyyun adawa inda suke neman ya sauka daga mukaminsa, saboda ya karya dokar kullen COVID-19 ya halarci taron da aka yi a lokacin da annobar cutar take ganiyarta.
A lokacin da yake mika sakon neman afuwarsa a zauren Majalisar Dokokin kasar, Mista Johnson ya ce ya dauki halartar taron a matsayin aiki na ma’aikatan fadar Downing Street.
Sai dai ya ce shi ma bai jin dadin yadda miliyoyin ’yan Birtaniya masu bin dokar zaman gidan yadda ya dace za su kalli karya dokar da ya yi ba.
Saboda haka, “Da wannan na ke neman afurwarku da kuma majalissa,” acewar Johnson.
Sai dai shugaban jami’iyyar adawa ta Labour, Keir Starmer, ya yi watsi da sakon neman afuwar yana mai cewa zancen banza Johnson din yake, kuma tsantsar rashin kunya ne ya fito yanzu ya nemi afuwar bayan watannin da aka shafe yana mai yaudarar mutane a kan maganar.
Wannan taron casu da Johnson ya halarta ya yamutsa hazo matuka inda da dama suka soki abin tare da wasu zarge-zarge a kai tun lokacin da aka gudanar da taron a 2020.