Finland ta tabbatar da niyyar shiga Kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO/OTAN ba tare da bata lokaci ba, inda ake sa ran kasar Sweden ta biyo baya, saboda firgita da mamayar da Rasha ke yi a Ukraine.
A ranar Alhamis ce kasar Finland ta tabbatar da niyyar shiga Kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO/OTAN cikin gaggawa, inda ake sa ran kasar Sweden za ta bi sahu.
- Hanifa ta Biyu: Yadda makwabci ya sace tare da kashe ’yar makwabcinsa
- Naira ta fadi warwas, ’yan sisaya na neman ta ido rufe
Kasashen biyu sun kasance ’yan ba ruwanmu kan shiga wani bangare na kawance soja tun bayan yakin duniya na biyu, sakamakon makwabtaka da tsohuwar Tarayyar Soviet.
Amma komai ya sauya sakamakon kutsen da Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya kaddamar a kan kasar Ukraine.
Tuni mahukuntan Rasha suka ce matakin shiga Kungiyar Kawancen Tsaron ga kasashen biyu na Finland da Sweden na zama barazana ga kasar ta Rasha kuma za ta mayar da martani, sai dai bata tantance irin matakin da za ta dauka ba.