Kocin tawagar ’yan ƙwallon ƙafar Super Eagles, Finidi George, ya yi murabus daga aikinsa bayan wata ɗaya da maye gurbin Jose Peseiro, a matsayin kocin tawagar.
Finidi ya tabbatar da ajiye aikin nasa ta kafar WhatsApp, inda ya tabbatar wa wakilinmu cewar ya ajiye aikin horarwar.
“Tabbas, da gaske ne na ajiye aikin,” ya tabbatar.
Finidi zai kasance mai horarwar da bai dauki lokaci ba a tarihin Super Eagles.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kocin ya gaza doke ƙasar Benin a wasan neman gurbin Kofin Duniya da aka yi a baya-bayan nan.
Da farko Najeriya ta yi kunnen doki da Benin a nan gida, yayin da kuma ta sha kashi da ci 2-1 a gidan Benin.
Rashin nasarar ya tayar da ƙura tsakanin magoya bayan Super Eagles da kuma masi sharhi kan harkar ƙwallon kafa a Najeriya.
Da dama dai na ganin Finidi George ba zai iya taɓuka abun a zo a gani ba, lamarin da ya sanya hukumar NFF yanke hukuncin fara neman mai horaswa daga waje.