✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fina-Finan Indiya 15 da aka hana nuna su a kasar

Masana’antar Fina-Finai ta Bollywood ita ce masana’antar fina-finai mafi girma wajen fitar da fina-finan da suka fi yawa a duniya a kowace shekara. Sai dai…

Masana’antar Fina-Finai ta Bollywood ita ce masana’antar fina-finai mafi girma wajen fitar da fina-finan da suka fi yawa a duniya a kowace shekara. Sai dai duk da yawan fina-finan da karbuwarsu akwai fina-finan da Hukumar Tace Fina-Finai ta kasar ta haramta sanyawa a gidajen sinimar kasar ko sayar da kasa-kasan bidiyonsu. Wadannan fina-finai sun hada da wadanda suke da maganganun batsa ko hotunan batsa ko wadanda suka saba wa al’adu ko suka shafi batun yankin Kashmiri ko addini.
Ga 15 daga cikin wadannan fina-finai da aka hana nuna su a kasar:
1. Bandit kueen (1994)
Bandit kueen an hana nuna shi ne saboda munanan kalaman da suke cikinsa da kuma nuna tsaraici.
2. Fire (1996)
Fim din Deepa Mehta wanda ya nuna rayuwar m adigo a tsakanin surukai mata biyu ta iyalan Indiya. Jarumai biyi na fim din, Shabana Azmi da Nandita Das da kuma daraktansa Deepa Mehta sun hadu da sakonnin barazanar kisa, kuma a karshe hukumar ta hana nuna fim din a kasar.
3. Kama Sutra – A Tale of Lobe (1996)
Shi ma fim din Kama Sutra – A Tale of Lobe ya hadu da fushin hukumar ce saboda batsa da nuna tsaraici da aka gina shi kan rayuwar wadansu masoya hudu a karni na 16 a kasar Indiya.
4. Urf Professor (2000)
Shi ma miyagun kalaman da aka yi amfani da su ne suka jawo aka haramta nuna shi.
5. The Pink Mirror (2003)
Shi kuma yana nuna yadda wadansu maza biyu da suka sauya halittarsu zuwa mata da wani dan luwadi suna kokarin tada sha’awar wani bako don yin lalata da shi.
6. Paanch (2003)
Paanch, fim ne na Anurag Kashyap wanda yake cike da tashin hankali da miyagun kalamai da shan miyagun kwayoyi. Kuma an gina shi ne kan kashe-kashen Joshi-Abhyankar na 1997.
7. Black Friday (2004)
Ya samo sunansa ne daga littafin Black Friday – The True Story of the Bombay Bomb Blasts na S Hussain Zaidi, wanda Anurag Kashyap ya mayar fim, ana ganin bai dace a sake shi a Indiya ba. Kuma wata Babbar Kotun Bombay t ace a dakatar da nuna shi saboda ba a kammala bincike da shari’a a kan harin bam na Bombay na 1993 ba.
8. Parzania (2005)
An hana nuna shi saboda ya tabo batun siyasa da ka iya tayar da zaune-tsaye a yankin Gujurat.
9. Sins (2005)
Sins Fim ne na batsa da ke nuna yadda wani shugaban addini ya fada tarkon wata mace har ya yi lalata da ita. Hakan ya fusata mabiya cocin Katolika bisa kukan cewa ya ci zarafin cocin. Sannan hukumar tace fina-finan ba ta amince da wuraren da suke nuna tsaraici ba, don haka aka haramta nuna fim din.
10. Water (2005)
Water wani fim ne na Deepa Mehta wanda ya tabo rayuwar wata bazawara a Indiya. Anurag Kashyap ya rubuta labarin wanda ya jawo zanga-zanga kuma masu tsattsauran ra’ayi kimanin dubu biyu suka lalata wurin da za a dauki fim din.
11. Firaak (2008)
Shi ma yana magana ne a kan rikicin yankin Gujarat, Firaak an ce ya ginu ne kan abin da yake faruwa a yankin Gujrat mai fama da yawan rikici, to amma ana ganin zai kara rura wutar rikcin da ke tsakanin mabiya addinin Hindu da Musulmi. Sai dai daga baya an amince a sake shi amma ya hadu da suka da caccaka daga masu sharhi.  
12. Gandu (2010)
Fim din Bengali ne da shi ma ya kunshi nuna tsaraic da batsa wadanda ake ganin sun saba wa al’adun mutanen Indiya.
13. Inshallah, Football (2010)
Inshallah, labara ne kan kwallon kafa kan wani yaro dan yankin Kashmiri da yake neman zuwa kasashen waje don zama kwararren dan kwallo. Sai dai an hana yaron fita daga kasar saboda an tuhumi mahaifinsa da aikata ta’addanci.
4. Dazed in Doon (2010)
Doon School daya ce daga cikin manyan makarantun kasar da ake girmamawa, amma sai aka rubuta labara a kan wani dalibin makarantar da hukumar makarantar ta koka cewa fim din zai zubar da kima da sunan makarantar.
15. Unfreedom (2015)
Fim ne day a kunshin madigo da labaran soyayya da kuma ayyukan ta’addanci da ake jingina wa Musulunci.
An cirato wannan bayani ne daga kafar labarai ta Intanet ta ScoopWhoop.