Domin sauke shirin latsa nan.
An jima ana takun saka tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finan Hausa, Kannywood, da wani bangare na al’umma bisa zarge-zarge ko korafe-korafe daban-daban.
Daya daga cikin zarge-zargen shi ne na bata tarbiya.
Ko me ya sa har yanzu masu harkar suka kasa sauya ra’ayoyin jama’a game da wannan zargi?
Ku biyo mu ku ji yadda Dokta Abdallah Usman Gadon Kaya ya yi ragargaza, da kuma yadda Ali Nuhu ya kare masana’antar.