✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Filin wasa na kasa da ke Legas ya shiga halin ni-’yasu

An gina filin wasa na kasa da ke Legas ne a shekarar 1972 kimanin shekaru 42 da suka gabata.  A wancan lokaci, yana daya daga…

An gina filin wasa na kasa da ke Legas ne a shekarar 1972 kimanin shekaru 42 da suka gabata.  A wancan lokaci, yana daya daga cikin filin wasan da ake alfahari da shi a Nahiyar Afirka.
Da farko an gina shi ne a matsayin wanda zai iya daukar ’yan kallo kimanin dubu 55 amma daga baya aka rage fadinsa ya koma yana daukar ’yan kallo su kimanin dubu 45.
Filin wasan yana kunshe ne da bangarori yin wasanni  daban-daban da suka hada da kwallon kwando da na tebur da daga karfe mai nauyi da guje-guje da tsallake da sauransu amma filin ya fi yin fice ne a bangaren wasan kwallon kafa.
A filin ne aka buga gasar cin kofin Nahiyar Afirka (Nations Cup) a shekarar 1980 a lokacin da Najeirya ta dauki nauyin gasar.  Sannan an yi amfani da filin wajen buga wasannin share fagen tafiya gasar cin kofin duniya a shekarun baya.
Haka kuma an taba amfani da filin wajen gudanar  da wasannin motsa jiki na Nahiyar Afirka (All-Africa Games) a shekarar 1973.
Sai dai abin bakin ciki shi ne yadda Gwamnati ta yi watsi da filin tun cikin shekarar 2002 watau kimanin shekaru 12 da suka gabata.  Hakan ta sa rabon da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta yi amfani da filin wasa tun a shekarar 2004.
Wannan halin ko-in-kula da gwamnati ta yi ga filin ta sa ya shiga mayuwacin hali.
Idan ka ziyarci filin a halin yanzu za ka tarar komai ya tabarbare hatta ciyayin da ke filin duk sun kone, kujeru sun kakkarye, rufin sama ya huje suna zubar da ruwa, shimfidar  wasannin guje-guje da tsalle-tsalle sun yage, babu wuta ko ruwa sannan daukacin ban dakin filin lalace.
Idan za a tuna a watan Janairun wannan shekarar ce Shugaban kasa Goodluck Jonathan ta hannun Tsohon Ministan Wasanni Bolaji Abdullahi ya yi yunkurin mayar da filin wasan ga kamfanoni masu zaman kansu don farfado da shi amma har yanzu babu wani canji da aka samu wajen farfado da filin daga mawuyacin halin da ya fada.