A kasa da kwana100 kafin a fara gasar cin Kofin duniya a Rasha, Hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) ta ce tana sa ran sayar da kimanin tikiti miliyan 1 da dubu 300 ga masu son kallon gasar a filayen wasannin da gasar za ta gudana a Rasha.
A wata sanarwar da ofishin hulda da jama’a na hukumar ya fitar a ranar Litinin da ta wuce an nuna hukumar ta ci gaba da sayar da tikicin a kashi na biyu daga ranar Talatar da ta gabata inda ta saki tikiti dubu 568 da 448. Sannan a shirin sayar da tikitin kashi na farko da ya gudana a tsakanin 5 ga Disamban 2017 zuwa 31 ga Janairun ta saki tikitin da yawansu ya kai dubu 735 da 168 ne wanda idan aka hada adadin za a samu tikiti Miliyan 1 da dubu 303 da 616 ke nan.
Sai dai Hukumar ta ce magoya bayan da za su fi cin moriyar sayen tikitin sun fito ne daga kasashe kamar haka: An ware wa mai masaukin baki Rasha tikiti dubu 197 da 832 sai Kolmbiya mai dubu 33 da 48 sai Peru da aka ware wa dubu 21 da 946, sai Jamus da aka ware wa tikiti dubu 21 da 639 sai Amurka mai dubu 20 da 347 sai Meziko mai dubu 18 da 155 sai Austireliya mai dubu 15 da 906 sai Ajantina mai dubu 15 da 214 sai Ingila mai dubu 14 da 890 sai Poland mai dubu 13 da 686.
Hukumar ta ce wadannan su ne kasashe 10 da aka fi ba fifiko wajen sayar musu da tikitin abin da ya yi saura ne za a sayar ga sauran kasashen duniya ciki har da Nahiyar Afirka.
Za a fara gasar cin Kofin Duniya a Rasha ne tun daga ranar 14 ga watan Yuni zuwa 15 ga watan Yulin bana. Kuma kasashe 32 ne ake sa ran za su fafata a lokacin gasar.
Jamus ce mai rike da kambun.