✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FIFA za ta inganta kwallon kafar mata a Saudiyya

Infantino ya ziyarci Saudiyya kan bunkasa kwallon kafar mata a kasar.

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) za ta taimaka wa kasar Saudiyya wurin inganta harkar wasan kwallon kafar mata a kasar.

Shugaban FIFA, Gianni Infantino ya bayyana hakan yayin ganawarsa da jami’an Sashen Kwallon Kafar Mata na Hukumar Kwallon Kafa ta Saudiyya (SAFF) a lokacin da ya ziyarci kasar.

Infantino ya kai ziyarar ce tare da Mataimakin Babban Sakataren FIFA Football Mattias Grafström.

A ziyarar tasu, shugabannin na FIFA sun gana da Ministan Wasannin Saudiyya, Yarima Abdulaziz bin Turki Al-Faisal da shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kasar (SAFF), Yasser bin Hassan Al-Misehal.

Sun kuma gana da jami’an hukumar da kuma ’yan wasa, inda suka jaddada muhimman ayyukan da Saudiyya ke yi na bunkasa kwallon kafar mata daidai da tsarin hukumar.