Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta bayyana niyyarta ta gina akalla filin wasa daya na zamani a kowace kasa da ke Nahiyar Afirka.
Shugaban Hukumar Gianni Infantino ne ya bayyana haka a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo lokacin da ya kai ziyara kasar don taya ta murnar cika shekara 80 da kafuwa da aka yi a karshen makon jiya.
Shugaban yana daga cikin shugabannin da hukumar ta gayyato don su taya ta murnar cika shekara 80 da kafuwa.
Shugaban ya ce hukumarsa za ta hada gwiwa ne da kamfanoni masu zaman kansu da masu hannu da shuni da ’yan kasuwa da masana’antu don ganin an tara akalla Dala biliyan daya (kimanin Naira biliyan 360) don gina filin wasan a kowace kasa da ke Nahiyar Afirka wanda hakan zai bunkasa harkar kwallon kafa a duniya.
Shugaban ya ce baya ga haka, hukumar za ta samar da kwararrun alkalan wasa a Nahiyar Afirka wadanda za su kasance masu cin gashin kansu da za su iya yin alkalanci a kowace gasa da hukumar ke shiryawa ba tare da shakkar komai ba.
Ya ce hakan zai sa a daina amfani da alkalan wasa wajen yin coge.