✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

FIFA ta jajanta wa Kano Pillars kan rasuwar tsohon dan wasanta

FIFA ta aiko da sakon ne ta bakin Shugaban NFF

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino ya jajanta wa kungiyar kwallon ta Kano Pillars dangane da rasuwar tsohon dan wasanta, Mohammed Bello Kofar Mata.

Shugaban hukumar ta FIFA ya aiko da sakon jajen ne ta hanyar wasika da ya aiko wa Alhaji Ibrahim Gusau, Shugaban Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) a ranar hudu ga watan Oktoban 2022.

“Cikin matukar bakin ciki da juyayi nake mika ta’aziyyata ta rasuwar Musa Bello Kofar Mata tsohon dan wasan kasa da kasa.

“A yayin da yake raye, ya buga wa kungiyar Super Eagles ya kuma buga kwallo a gasar wasan cin kofin duniya ’yan kasa da shekara 20 na FIFA”

“A madadin ni kaina da kuma dukkanin ’yan wasan kasa da kasa, ina mika ta’aziyyata ga hukumara NFF da iyaye da ‘yan uwa da iyaklin marigayin da kuma dukkannin masoya marigayin.” In ji shugaban FIFA, a cewar Leadership.

Kafin rasuwarsa, Muhammad Bello Kofar Mata ya buga wa kungiyar Buffalo da Kano Pillars wasa har sau biyu, sannan ya buga wa kungiyoyin Ifeanyi Uba da El-Kanemi. Ya kuma wakilci Najeriya a wasannin kasa da kasa.