Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA, ta fitar da jerin ’yan wasa da kwararrun masu buga tamaula suka zaba mata a matsayin tawagar fitattun ’yan wasanta na shekara.
FIFA ta sanar cewa kimanin kwararrun ’yan kwallon kafa 19,000 ajin maza ne suka zabi tawagar fitattun ’yan wasan 11 a matsayin zakarun gwajin dafi na shekarar 2021.
Wannan ita kadai ce kyautar da ake bayarwa wadda kwararrun masu taka leda ne kadai ke zaba, inda kuri’un ke fitowa daga kowace nahiyya ta duniya.
Tawagar ta shekarar 2021 ta kunshi Gianluigi Donnarumma na AC Milan/Paris Saint-Germain da kasar Italiya a matsayin mai tsaron raga.
Masu tsaron baya kuma sun hada da David Alaba (Bayern Munich/Real Madrid, Austria) da Leonardo Bonucci (Juventus, Italiya) da kuma Ruben Dias (Manchester City, Portugal)
A bangaren ’yan tsakiya masu tare akwai Kevin De Bruyne (Manchester City, Belgium) da Jorginho (Chelsea, Italiya) da kuma N’Golo Kante (Chelsea, Faransa).
Gwarzon dan wasan duniya na FIFA Robert Lewondoski na Bayern Munich da Poland, shi ya ja ragamar wanda kwararrun ’yan kwallo suka zaba a matsayin fitattun ’yan wasan gaba.
Sauran fitattun ’yan wasan gaba sun hada da Erling Haaland (Borussia Dortmund, Norway) da Lionel Messi (Barcelona/Paris Saint-Germain, Argentina) da kuma Cristiano Ronaldo (Juventus/Manchester United, Portugal).