A shekatranjiya Laraba ne Hukumar shirya kwallo ta duniya FIFA ta bayar da sanarwar dage Najeriya daga shiga harkokin wasanni har sai abin da hali ya yi. Hukumar ta yi haka ne bayan ta dibar wa kasar wa’adin ranar Talatar da ta wuce da ko dai ta mayar da shugaban Hukumar kwallon kafa ta kasa NFF Alhaji Aminu Maigari da wata kotu ta bayar da umarni aka tsige shi a karshen makon jiya ko kuma ta dauki mataki. Har wa’adin ya cika gwamnati ba ta bi umarnin FIFA ba da hakan ya sa ta dage kasar daga shiga duk harkokin wasanni.
Sai dai FIFA ta ware wa Najeriya zuwa ranar 15 ga watan nan da muke ciki da lallai ta sasanta a kan dambarwar shugabancin NFF ko kuma a hana ta halartar gasar cin kofin duniya na mata na ’yan kasa da shekara 20 da zai gudana a Kanada daga ranar 5 ga watan Agusta mai zuwa. Kenan akwai yiwuwar FIFA ta yafewa Najeriya muddin ta sasanta akan dambarwar shugabancin nan da 15 ga watan nan da muke ciki.
Wannan dagewar da aka yi wa Najeriya zai kasance babu wani jami’in da ke kula da harkar kwallo a Najeriya da zai iya halartar taron da FIFA za ta yi a ko’ina a ciki da wajen kasa. Sannan babu wani kulob daga kasar nan da zai halarci kowace irin gasar kwallo da hukumar ta shirya a duk fadin duniya.
Ana zargin gwamnatin Najeriya na da hannu wajen tsige shugaban hukumar NFF, Alhaji Aminu Magairi ne jim kadan bayan komawa gida bayan an fitar da kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Brazil. Gwamnati ta zarge shi ne da laifin yin magudi a wajen biyan ’yan kwallon Najeriya a yayin gasar.
FIFA dai ta ki amincewa da nadin da Ma’aikatar matasa da wasanni ta yi na sabon shugaba a hukumar NFF, kuma ta sha alwashin ba za ta amince da shi a matsayin shugaban Hukumar ba.
A wani labarin kuma Kamfanin nan da ya shahara wajen tallafawa Najeriya da kayayyakin kwallo fiye da shekaru goma da suka wuce kawo yanzu, a ranar Litinin da ta gabata ne ya bayar da sanarwar dakatar da cigaba da tallafa wa Najeriya a bangareb sanar da kayayyakin wasanni har sai baba-ta-gani saboda tsige shugaban Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) Alhaji Aminu Maigari tare da daukacin membobin hukumar.
Idan za a tuna, wata kotu ce da ke Jos ta bayar da umarnin tsige shugaban hukumar Alhaji Aminu Maigari tare da daukacin membobinsa a wani hukunci da ta yanke a makon jiya al’amarin da bai yi wa kamfanin da kuma Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA dadi ba. Hasalima ita kanta Hukumar FIFA ta dibar wa Najeriya wa’adi don sake komawa da Aminu Maigari kan mukaminsa ko kuma ta dauki mummuman mataki a kan Najeriya. Matakin zai hada da dakatar da Najeriya daga shiga kowace irin gasa da hukumar za ta shirya a fagen kwallon kafa. Sannan Hukumar FIFA ta kara da cewa za ta umarci ita ma Hukumar kula da kwallon kafa a Afirka (CAF) ta dage Najeriya daga shiga kowace irin gasa da za ta shirya da zarar FIFA ta dauki matakin.
FIFA ta dakatar da Najeriya bisa katsalandar din gwamnati a harkar kwallo
A shekatranjiya Laraba ne Hukumar shirya kwallo ta duniya FIFA ta bayar da sanarwar dage Najeriya daga shiga harkokin wasanni har sai abin da hali…