✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FIFA ta ci tarar Najeriya Naira Miliyan 11

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (FIFA) ta ci tarar Najeriya Dala Dubu 31 wanda ya yi daidai da Naira Miliyan 11 saboda sakacin da ta…

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (FIFA) ta ci tarar Najeriya Dala Dubu 31 wanda ya yi daidai da Naira Miliyan 11 saboda sakacin da ta yi wajen barin magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles suka mamaye filin wasa na Godswill Akpabio da ke garin Uyo a wasan da Najeriya ta lallasa Kamaru da ci 4-0 a gasar neman zuwa gasar cin kofin duniya da aka yi a watan jiya.  Magoya bayan kungiyar sun mamaye filin wasan ne jim kadan bayan an tashi wasan, da hakan ya saba wa dokar Hukumar kwallon kafa ta duniya.

FIFA ta ce saboda wannan sakaci da ta yi har magoya bayan kungiyar suka mamaye filin wasan jim kadan bayan an tashi wasan ne ya janyo ta dauki wannan mataki.

Idan za a tuna Hukumar ta taba cin tarar Najeriya makudan kudi saboda yadda magoya baya suka cika filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna fiye da kima a wasan da Super Eagles ta yi da kasar Masar a gasar neman zuwa gasar cin kofin Afirka a shekarar 2016.