Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta sanar da kasashen Marocco da Portugal da Spain cewa su za su karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2030.
Sai dai FIFA ta ce za a yi wasanni uku na farkon gasar a kasashen Argentina da Paraguay da kuma Uruguay albarkacin cika shekara 100 cif-cif da fara gasar a lokacin.
Sanarwar wacce hukumar ta yi a ranar Laraba na nufin cewa za a gudanar da gasar ce a kasashe shida da ke nahiyoyi uku.
“FIFA ta amince da murya daya cewa za a gudanar da gasar ce ta hadin gwiwa a kasashen Morocco, Portugal da Spain a shekara ta 2023,” kamar yadda FIFA ta bayyana a cikin sanarwar.
“Bugu da kari, “la’akari da tarihin gasar da aka fara gudanarwa ta cin kofin duniya, hukumar gudanarwar FIFA ta kuma amince da murya daya cewa za a buga wasanni ukun farko na gasar a kasashen Uruguay, Argentina da Paraguay.”