Kwamitin Gudanarwar Jam’yyar PDP na kasa (NWC), ya ba da sanarwar rushe shugabancin jam’iyyar a Jihar Kano da ke goyon bayan tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Matakin na zuwa ne bayan umarnin da wata babbar kotu da ke Abuja ta bayar na hana jam’iyyar daukar matakin rushe shugabancin da ke karkashin jagorancin Shehu Wada Sagagi.
- NNPC ya fi kowane kamfanin mai a duniya yin harkokinsa a fili
- Na kadu matuka da harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna — Buhari
A sanarwar da ta fitar ta hannun sakataren tsare-tsare na jam’iyyar, Umar M. Bature, PDP ta ce sun yi la’akari da sashe na 29(2)(b) da kuma sashe na 31(2)(e) wanda ya bai wa jam’iyyar damar rushe shugabancinta.
Sannan jam’iyyar ta ce ta kafa kwamitin rikon kwarya a jihar karkashin jagorancin Alhaji Ibrahim Atta, da sakatarenta Barista Baba Lawan, yayin da Ibrahim Aminu Dan Iya, Hajiya Ladadi Dangalan, Aminu Abdullahi Jingau, Muktar Janguza da Abdullahi Isah Sulaiman suke a matsayin mambobi.
PDP ta rushe shugabancin ne bayan ficewar Sanata Kwankwaso daga jam’iyyar a ranar Litinin, inda ta zargi wasu magoya bayansa da neman yi mata sakiyar da ba ruwa.