✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FC Barcelona za ta hadu da Leicester City

Kulob din FC Barcelona ya ce zai hadu da kulob din Leicester City na Ingila wanda ya lashe gasar rukunin firimiar Ingila ta bana ne…

Kulob din FC Barcelona ya ce zai hadu da kulob din Leicester City na Ingila wanda ya lashe gasar rukunin firimiar Ingila ta bana ne a wasannin sada zumunta da kulob din zai gudanar a watan Agusta mai zuwa a shirye-shiryen tunkarar kakar wasa mai zuwa.  Kulob din ya ce zai kara da na Leicester City ne a filin wasa na Stockholm ne a ranar 3 ga watan Agustan wannan shekara.
Kulob din ya ce baya ga Leicester City, zai kuma kara da kulob din Liberpool da na Celtic dukkaninsu da ke Ingila.  Kulob din ya ce zai kece raini ne da kulob din Celtic a ranar 30 ga watan Yuli a Dublin, yayin da zai hadu da na Liberpool a ranar 6 ga watan Agusta, watau kwana uku bayan ya hadu da na Leicester City, sai dai bai ambaci filin wasan da za su kara da na Liberpool din ba.
Kawo yanzu FC Barcelona ce take saman tebur a gasar La-Liga ta Sifen da maki 88 yayin da kulob din Real Madrid yake biye da maki 87 kuma dukkan kungiyoyin gobe ne za su yi wasanninsu na karshe don tantance kungiyar da za ta daga kofin na La-Liga.