Hukumar Bincike ta Amurka (FBI) na binciken musabbabin mutuwar wani bakar fata da wani bidiyo ya nuna yadda wani dan sanda farar fata ya tattake masa wuya.
Bidiyon da ya karade gari ya nuna mutumin mai shekara 40 yana kururuwar neman dauki a sadda wani dan sandan farar fata ya take masa wuya.
Hukumar ‘yan sanda a jihar ta Minnesota ta ce tuni ta dukufa binciken lamarin don gano halikanin gaskiya.
Lamarin dai ya kara janyo kakakausan suka daga masu fafutuka kan zargin da ake wa ‘yan sanda na muzguna wa bakaken fata a Amurkan.
- Dokar kulle: Yadda mutum 875 suka kashe kansu a Nepal
- El-Rufai ya sauya dokar kullen coronavirus
- Ma’aikatan jinyar masu COVID-19 sun tafi yajin aiki
Shugaban ‘yan sanda a jihar ta Minnesota, Jacob Frey ya bayyana wa ‘yan jarida lamarin a matsayin abin takaici matuka wanda ba za su lamunta ba.
Ya ce, “Na yarda da abin da na gani kuma abin takaici ne ta kowacce fuska. Bai dace a rika cin zarafin mutane a Amurka kawai saboda launin fatarsu ba.
Wannan dai yana cikin zarge-zargen da a baya-bayan nan ake wa ‘yan sandan na Amurka na muzgunawa tare da cin zarafin bakaken fata a kasar.
Ko a kwanaki ma sai da aka zargi wani jami’in dan sanda a jihar Maryland da harbe wani mutum har lahira a kan motarsu ta sintiri.