Wani Limamin Coci da ke zaune a Jihar Kano ya amsa laifin da ya aikata na yi wa tagwaye ’yan shekaru 13 da wata ’yar’uwarsu fyade yayin da aka gurfanar da shi a gaban kotun Majistari a jiya.
Mai Magana da Yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Magaji Musa Majia ya gabatar da Fasto Samuel Joe, Limamin Cocin da ke zaune a kan titin Wazahed a cikin Unguwar Sabon Gari da ke cikin Karamar Hukumar Fage a Jihar Kano tare da wasu mutum 34 da ake zargi da aikata laifin fyade.
Takardar karar kotun ta nuna cewa Mista Joe ya yaudari ’yan matan ne inda ya yi amfani da su a lokaci daya a kan gadon matarsa sannan a lokaci guda kuma ya rika sanya dan yatsa a farjin daya yarinyar.
Yayin da aka karanta masa laifinsa da ake tuhumarsa da aikatawa sai ya amince da laifinsa inda ya dora alhakin a kan shedan.
Daga nan sai Alkalin kotun, Mai Shari’a Maryam Ahmad Sabo ta bayar da ummarnin a tsare shi a gidan yari daga bisani ta dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Satumban shekarar 2017.