566. An karbo daga Is’hak ya ce: “Habban ya ba mu labari ya ce, Hammam ya ba mu labari, ya ce, “kattada ya ba mu labari daga Abu Khalil daga Abdullahi dan Haris daga Hakim dan Hizam (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Hakika Annabi (SAW) ya ce, “Mai saye da sayarwa suna da zabi har sai sun rabu.” Ya ce, “Hammam ya ce, “Na samu a cikin littafina cewa, “Mai saye da mai sayarwa suna da zabin cinikin har sau uku, idan suka yi wa juna gaskiya suka bayyana aibi sai a sanya musu albarka a cikin cinikinsu. Idan suka yi wa juna karya kuma suka boye aibin kaya, mai yiwuwa a yi riba amma za a cire musu albarkar cinikinsu.” Ya ce, “Hammam ya ba mu labari, ya ce, Abu Tayyah ya ba mu labari cewa: “Lallai shi ya ji Abdullahi dan Haris yana ba da labari da wannan hadisi daga Hakim dan Hizam daga Annabi (SAW).
Babi na Arba’in da Takwas:
Idan mutum ya sayi wani abu kuma ya yi kyauta da shi ga wani a wannan lokacin kafin su rabu da mai sayarwa. Ko mai sayarwar bai yi musu ba, idan mutum ya sayi bawa ya ’yanta shi.” dawus ya ce, “Wanda ya sayi kaya bisa yarda sa’an nan ya sayar, cinikin ya halatta kuma ribar ta halatta.” Humaidiyyu ya ce, “Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Amru ya ba mu labari daga dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Mun kasance tare da Annabi (SAW) a cikin wata tafiya, sai na kasance cikin mahaya a bisa wani rakumin Umar mai wahalar sha’ani. Sai ya kasance yana rinjayata, yana gabatar mutane Umar na tsawatar da shi, ya mayar da shi baya. Sa’an nan ya sake gabata Umar ya tsawatar da shi ya mayar da shi. Sai Annabi (SAW) ya ce, wa Umar: “Ka sayar mini da shi.” Ya ce, “Ai shi naka ne ya Manzon Allah!” Ya ce, “Ka sayar mini da shi! (ba kyauta ba).” Sai Manzon Allah (SAW) ya saye shi, kuma Annabi (SAW) ya ce, “Na ba shi ga Abdallahi dan Umar ka aikata abin da kake so da shi.” Abu Abdullahi ya ce, “Laisu ya ce, Abdurrahman dan Khalid ya ba ni labari daga dan Shihab daga Salim dan Abdullahi daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Na sayar da filina na Khaibara ga Sarkin Muminai Usman dan Affan (RA) bisa wani filinsa a Wadi (sunan wuri kusa da Madina). Lokacin da muka kulla ciniki sai na koma bisa duddugena da sauri har na fita daga gidansa domin tsoron kada ya warware (fasa) cinikin. Saboda Sunnah ta kasance cewa, lallai mai saye da mai sayarwa suna da zabi har sai sun rabu.” Abdullahi ya ce, “Lokacin da cinikina da tasa suka wajaba sai na fahimci lallai ban kyauta wa shi (Usman) ba, saboda na kai shi kusa da kasar Samudawa da kamar tafiyar darare uku. Kuma shi ya matso da ni kusa da Madina da kamar tafiyar darare uku.”
Babi na Arba’in da Tara: Abin da aka hana game da yaudara a cikin ciniki:
567. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abdullahi dan Dinar daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: “Lallai wani mutum ya ambata wa Annabi (SAW) cewa, hakika shi ana yaudararsa a cikin ciniki. Sai (Annabi) ya ce, “Idan za ka yi ciniki ka rika cewa, “Ban da yaudara.”