✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fasinjoji sun yi curko-curko bayan direbobin Adaidaita Sahu sun tsunduma yajin aiki a Kano

Suna yajin aikin ne saboda dokar sabunta lasisin tuki da KAROTA ta kirkiro.

A Jihar Kano, dubban daruruwan fasinjoji ne suka yi curko-curko a kan tituna bayan da direbobin babura masu kafa uku da aka fi sani da Adaidaita Sahu suka tsunduma yajin aiki ranar Litinin.

Sun yajin aikin ne don nuna rashin amincewarsu da matakin da Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar (KAROTA) na tilasta musu sake sabunta lasisin tuka baburan a Jihar.

Aminiya ta lura cewa a sakamakon karancin baburan, wadanda sune kaso mafi yawa na hanyoyin sufuri a Jihar, mutane da dama sun koma tafiya a kafa, wasu kuma na amfani da kananan motocin daukar kaya wajen sufurin.

Kazalika, wasu kuma sun koma amfani da motocin bas-bas da na tasi da a baya aka rage amfani da su a cikin birnin na Kano sakamakon mamayar Adaidaita Sahun.

Hukumar ta KAROTA dai ta ce tilas ne direbobin su sabunta lasisin tukin a kan N8,500, sai kuma sabo a kan N18,000, kuma dokar ta fara aiki ne daga ranar daya ga watan Janairun sabuwar shekara, kamar yadda Shugaban hukumar, Baffa Babba Dan-Agundi ya tabbatar.

A cewar kungiyoyin direbobin baburan, yarjejeniyar da suka cimma da hukumar ita ce babu batun sabunta lasisin a duk shekara, kamar yadda suka amince.

Ko a watan Fabrairun bara ma, sai da direbobin Adaidaita Sahun suka yi yajin aikin kwana uku saboda harajin N100 kullum da hukumar ta fara karba a hannunsu.