✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fashin zuwa aiki ya janyo wa ’yan NYSC 5 maimatawa a Sakkwato

Uku daga ciki za su sake ne baki daya, saboda sun ki zuwa kauyukan da aka tura su

Shugaban Hukumar Yi Wa Kasa Hidima na Jihar Sokoto (NYSC) Muhammad Nakamba ya ce an kara wa biyar daga cikin wadanda aka tura jihar wa’adin aiki, sakamakon fashi zuwa aiki.

Ya bayyana hakan ne yayin faretin yaye masu yi wa kasa hidima a ranar Alhamis, inda ya ce uku daga ciki za su sake ne baki daya, saboda sun ki zuwa kauyukan da aka tura su.

Sauran biyun kuma za a kara musu watanni ne, bisa fashin zuwa aiki, abin da ya ce ba za su lamunta ba.

Nakamba ya ce jimillar masu yi wa kasa hidimi 537 ne jihar ta yaye, kuma biyu daga ciki sun samu kyautar karramawa daga Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, bisa gudummawarsu ga  kauyukan da asuka yi aiki.

Haka kuma ya yi godiya ga Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal bisa gudummawarsa ga shirin, musamman sanya wa daliban alawus din wata-wata da ya yi, bayan na tarayya da ake ba wa kowannensu.

A cewarsa, shirin ya tura akasarin masu yi kasa hidimi da suka karanci fannin kiwon lafiya zuwa yankunan karkara, matakin da ya ce zai taimaka matuka wajen magance matsalar karancin ma’aikata a fannin a jihar.