Rundunar ‘Yan Sandan Legas ta ce fashin da aka yi a gidan dan takarar shugaban kasa a shekarar 1993, Cif MKO Abiyola da na gida a ka shirya.
Da sanyin safiyar Laraba 2 ga watan Satumba wasu ‘yan fashi suka shiga gidan Marigayi MKO Abiola da ke Ikeja a Legas, suka yi awon gaba da kudi da gwalagwalai.
A sanarwar da iyalan MKO suka fitar wacce dansa Tundun Abiola ya sanya wa hannu sun ce ‘yan fashin sun jefa su cikin firgici da fargaba, sun ci zarafinsu suka kuma sace musu dukiya da kadarori masu yawa.
Suka ce ba a sami salwantar rai a harin da ‘yan fashin suka kai musu ba.
Sai dai Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar Legas DSP Bala Elkana ya ce ba ‘yan fashi da makami ba ne suka far wa gidan na Abiola, sai dai wasu bata-gari ne suka haura gidan, kuma da akwai alamu da na gida aka hada baki aka yi fashin.
Ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Legas Hakeem Odumosu ya ziyarci gidan iyalan Abiola tare da jami’an tsaro, “an kama wasu da ake zargi da hannu a fashin, ana kuma ci gaba da bincike”, inji shi.
A nasa bangaren Kwamishinan ‘Yan Sandan Legas CP Hakeem Odumosu ya ce ta karkashin wani rami da ke daura da gidan ‘yan fashin suka shiga gidan da ke yankin Opebi a Ikeja Babban birnin jihar Legas.
“Mutum uku ne suka yi fashin kuma mutum daya ne cikin su ukun yake rike da makami.
“Mun kara tsara tsaro a yankin muna kuma ci gaba da bincike a kan wadanda muka kama”, inji shi.
Gidan da ‘yan fashin suka kai harin gida ne na Cif MKO Abiola mutumin da ya lashe zaben shugaban kasa a shekarar 1993 a jam’iyyar SDP, bayan ya kada abokin karawarsa Alhaji Bashir Othman Tofa na jam’iyyar NRC; zaben da tsohon Shugaban Kasa na mulkin soji Janar Ibrahim Badamasi Babangida (Murabus) ya soke.