Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta bayyana kujerar Dan Majalisa mai wakiltar Sabon Gari, Aminu Abdullahi Shagali a matsayin wadda babu kowa a kanta.
Majalisar ta ce ta dauki matakin ne saboda Aminu Shagali wanda shi ne tsoho Shugabanta ba ya halartar zama ko wasu harkokin Majalisar.
- ’Yan bindiga sun saki sabon bidiyon daliban Kwalejin Afaka
- An kai wa unguwar Hausawa hari a Imo
- Yadda El-Rufa’i ya caccaki Jonathan kan sace ’yan matan Chibok amma ya ki tattaunawa a sako daliban Kaduna
Zaman Majalisar na ranar Talata wanda Mataimakin Shugabanta, Isaac Auta Zankhai ya jagoranta ya kuma tsawaita dakatarwar da ta yi wa wasu ’ya’yanta hudu zuwa wata 12.
Wadanda aka tsawaita dakatarwar da aka yi musu su ne: Mukhatar Isa Hazo, Mazabar Basawa; Salisu Isa, Mazabar Magajin Gari; Nuhu Goro Shada Lafiya, Mazabar Kagarko; da kuma Yusuf Liman, Mazabar Makera.
Ta kuma umarci akawunta da ya sanar da wadanda matakan suka shafa game da matsayin da zauren Majalisar ya dauka.
A watan Fabrairun 2020 ne Aminu Shagali ya sanar da saukarsa daga kujerar Shugaban Majalisar bisa dalilai na kashin kansa, amma wasu rahotanni na cewa wasu ’yan Majalisar ne ke neman tsige shi.