Rundunar tsaro ta NSCDC a jihar jigawa, ta ce mutum biyar ne suka jikkata sakamakon fashewar tukunyar Gas da aka yi kokarin yin fasa-kaurinsu zuwa jihar.
Kakakin rundunar a jihar CSC Adamu Shehu ne ya bayyana hakan a Dutse babban birnin jihar, inda ya ce shaguna da gidaje da dama sun kone sanadiyar hakan.
- Wani mutum ya kashe ma’aikacin gidan mai saboda kin sayar da barasa
- Zabar PDP JIhadi ne a Katsina —Lado
Kakakin ya kara da cewa lamarin ya auku ne ranar Litinin da karfe 9:00 na dare, bayan jami’an tsaron da ke aiki a shingen bincike suka dakatar da babbar motar mai dauke da tukunyar gas guda 25.
Ya ce, “Direban ya ki tsayawa bayan an tsaida shi, hakan ne ya sanya jami’an tsaron suka bi shi a baya.
“Sakamakon hakan, guda daga tukunyar ta fado daga motar ta fashe, take kuma ta kama da wuta,” inji shi.
Kakakin ya kuma ce motar ta taso ne daga garin Tinkim da ke karamar kukumar Magarya, inda ta nufi Hadeja.
“Tuni an kai wadanda suka samu raunin asibiti domin karbar magani”, in ji Adamu.
A nasa bangaren, Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar DSP Lawan Shi’isu ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce shagubna 17 ne da gidaje biyar suka kone.