Akalla mutum 20 sun jikkata a sanadiyyar fashewar tukunyar iskar gas a unguwar Sheka da ke Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.
Wani mazaunin unguwar, Malam Idi ya ce shaguna da dama sun kone a sakamakon tashin wutar bayan tukunyar gas din ta yi bindiga a wani shagon sayar da gas din girki.
- Kotu ta daure matashi shekara 10 bisa yi wa yarinya fyade
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Matasan Najeriya Ke Raina Jari
“Mutum 20 ne lamarin ya ritsa da su, kuma an garzaya da su zuwa asibiti,” a cewar kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif.
Malam Idi ya ce yawanci mutanen da wutar ta kama suna shagon sayar da gas din girkin ne, da kuma masu shagunan da ke kusa da wurin.
Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif, ya ce lamarin ya auku ne a ranar Alhamis da dare, a dalilin wani mutum da ke suyan kifi a kusa da shagon gas din.