Akalla mutum 11 ne suka mutu, cikinsu har da almajirai uku sakamakon fashewar wata tankar dakon man fetur da ta yi bindiga a yankin Gawu na Karamar Hukumar Abaji a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ba a kai ga tantance sunan almajiran ba dai kawo yanzu, amma ragowar mutanen sun hada da wata matar aure mai suna Halima Mohammed Yusuf, Shugaban ’yan Kato-da-gora na yankin Gawu, Adamu Ibrahim.
- Yadda ’yan bindiga ke samun miyagun kwayoyi a Sakkwato — Tambuwal
- Za mu shirya mukabala tsakanin Abduljabbar da Malamai — Ganduje
Sauran sun hada da Dantala Usman da Umar Aliyu da Mohammed Hamza da Hassan Usman da Gambo Hamisu da kuma Sani Abdulmutalib.
Wani mazaunin yankin mai suna Usman Yakubu ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na safiyar Lahadi, a daidai lokacin da tankar ke kokarin kauce wa yin karo da wata babbar motar dakon kaya.
A cewarsa, wasu mazauna yankin, bayan lura da cewa man fetur na ta zuba a kasa sai mutane suka rika fitowa da jarkoki da bokitai domin kwasar ganima.
“Man da yake malala ne ya kama da wuta tare da kashe almajirai uku da wasu karin mutum takwas, ciki har da wata mata da ta zo domin korar almajiran daga wajen,” inji shi.
Dagacin yankin na Gawu, Alhaji Yusuf Ibrahim ya ce, “Abin takaici, wata mata ita ma ta rasa ranta a kokarin korar yaran daga wurin. Tuni aka yi jana’izarsu duka kamar yadda addinin Musulunci ya tanada,” inji shi.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) shiyyar Abuja, Wobin Gora ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar salula.
Ya ce mutane 11 sun kone kurmus, yayin da wasu mutum 10; maza takwas da mata biyu da suka samu kuna a jikinsu kuma aka garzaya da su asibiti don ci gaba da samun kulawa.