✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fashewar ‘nakiya’ ta kashe mutum 2 a Kaduna 

Ana zargin 'yan ta'adda ne suka dasa bam a hanyar da mutanen suka bi.

Wasu mutum biyu sun mutu yayin da wani abu da aka binne ya fashe ya kuma tashi da su a Karamar Hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na yammacin Alhamis.

Motar wadanda abin ya rutsa da su ta bi ta kan abin fashewar da ake zargin ’yan ta’adda ne suka dasa a Zangon Tofa a yankin Kabrasha.

An rawaito cewa mutanen kauyen na jigilar amfanin gonar da suka girbe lokacin da lamarin ya afku.

Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ayyana mutum biyu a matsayin wadanda suka rasa rayukansu; Babajo Alhaji Tanimu da Safiyanu Ibrahim.

A cewarsa, Gwamnatin Jihar na bincike kan lamarin.

Ya kuma ce Gwamnan Jihar, Nasiru El-Rufai, ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa.