An shiga rudani a mahadar Yazufa Danmani da ke yankin Rigasa a Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, yayin da wani abu da ake zargin bam ne ya raunata mutum uku.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru da misalin karfe 8:30 na daren ranar Juma’a kusa da wani shagon hada-hadar kudi na POS da ke daura da masallacin Abubakar Sadiq.
- Koriya ta Arewa na da makaman da ba a san adadinsu ba —Amurka
- Taron APC: Hadin kai ko dinkin gangar auzunawa?
Aminiya ta gano abin da ya fashe an dasa shi ne kusa da babur din shagon da ake hada-hadar kudin na POS.
Wani dan banga a yankin da ya bukaci sakaya sunansa, ya ce mai shagon POS ya ji mummunan rauni amma an garzaya da shi asibiti.
“An garzaya da shi asibiti saboda hannunsa da kafarsa sun samu munanan raunuka.
“An sanar da ’yan sanda faruwar lamarin,” a cewarsa.
Wani mazaunin yankin da ya bayyana kan shi da suna Shehu ya ce mutum uku ne suka ji rauni sakamakon fashewar abun.
A cewarsa jami’an da ke cire bam sun isa yankin kuma sun yi nasarar cire wani bam da aka dasa wanda bai tashi ba.
“Daga cikin wanda suka ji rauni har da mai shagon POS, ya ji rauni sosai amma ragowar ba su ji jiki ba kamar shi,” inji shi.
Aminiya ta rawaito yadda Kwamishinan tsaron cikin gida na Jihar, Samuel Aruwan, ya gargadi jama’ar jihar su kasance masu sanya ido, saboda akwai rahoton cewar ’yan ta’adda na fara shirin kai hare-hare ta hanyar dasa bam a wuraren ibada da kasuwannin da ke jihar.