✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fari ya kashe dabbobi miliyan daya a Habasha —Rahoto

Mutum fiye da miliyan takwas na fuskantar matsalar karancin abinci a Habasha.

Rahoton Kungiyar ’Yan Gudun Hijira ta Kasa da Kasa (IOM) ya nuna cewa, dabbobi sama da miliyan daya da rabi ne suka mutu sakamakon matsalar fari a wasu sassan kasar Habasha.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, a baya-bayan nan wasu yankunan Habasha na fuskantar fari, lamarin da ya yi sanadiyar fuskantar matsalar karanci abinci ga mutum sama da miliyan takwas da kuma mutuwar dabbobi kimanin milyan daya da rabi.

“Kusan mutum 300,000 da matsalar farin ta shafa suka yi kaura zuwa wurare daban-daban don neman ruwa da wurin kiwon dabbobi,” inji rahoton IOM.

A nata bangaren, Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana kokarin tallafa wa wadanda matsalar ta shafa da abinci da matsugunin gaggawa da sauran abubuwan bukata da suka hada da ruwa mai tsabta, dakunan shan magani da sauransu domin daidaita musu rayuwa.

A ranar Alhamis da ta gabata Ofishin Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya (UNOCHA) ya ce akalla dabbobi miliyan bakwai ne suka mutu sakamakon fari a tsakanin wasu kasashen Afirka.

Ofishin ya yi gargadin yanayin ka iya tsananta saboda hasashe ya nuna mai yiwuwa a rasa ruwan saman da aka saba samu a Oktoba zuwa Disamba a yankun da lamarin ya shafa.

Ya kara da cewa, ana fargabar fama da matsalar yunwa sakamakon rashin samun ruwan sama yadda ya kamata a wasu sassan Habasha da Kenya da kuma Somaliya.

(NAN)