Mazauna Jihar Ondo sun shiga rudani bayan bankuna sun rurrufe saboda fargabar kai musu hari sakamakon karancin sabbin kudi.
Wasu daga cikin bankunan da suka ki budewa a ranar Laraba sun hadar da bankin Zenith da Access da Polaris da WEMA da Unity da kuma First Bank a Akure, babban birnin Jihar.
- Babu gudu ba ja da baya a kan ranakun zaben 2023 – Yakubu
- IMF ya shawarci CBN ya kara wa’adin daina karbar tsofaffin kudi
Rahotanni sun nuna cewar bankunan kasuwancin sun ki budewa ne biyo bayan fargabar da aka shiga, wanda hakan ta sanya wasu kwastomomi kai wa wasu bankuna hari a fadin kasar nan.
Bankin WEMA da ke yankin Adegbola a Akure ya yi ta maza ya bude reshen nasa, amma an girke jami’an tsaro don gudun ko ta kwana.
Wasu daga cikin kwastomomin sun buga sammako tun misalin karfe 6:30 ka safe suka isa bankin da nufin cire kudi.
Sai dai kwastomomi sun fara yamutsa hazo biyo bayan gaza samun kudi a injinan ATM sannan bankin ya ki budewa domin bai wa mutane damar shiga ciki don cire kudi.
Wasu daga cikin fusatattun kwastomomi sun yi yunkurin shiga bankin ta karfin tsiya amma jami’an tsaro sun hana su tare da kwantar musu da hankali.
Shi ma bankin Polaris da ke yankin haka kwastomomi suka yi masa cuncirundo tun da duku-dukun safiya da nufin cire kudi amma babu wani bayani.
Wasu kwastomomi a Ibadan haka suka fasa bankuna tare da yi musi barna sakamakon gaza basu kudi da wasu bankuna suka.
Ana ci gaba da samun tarzoma biyo bayan cajin kudi da takaita cire kudi da Babban Bankin Najeriya (CBN), ya yi.