Biyo bayan sanarwar dakatar da wasannin rukunin gasar La Liga da ma rukunin na biyu ta Sifaniya na a akalla makonni biyu, kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta tsaurara matakan kariya da gwaje-gwaje saboda kiyaye yaduwar cutar Korona.
Hukumar gasar ta La Liga dai sun dauki matakin ne bayan an kebe wani babban ma’aikacin kungiyar Real Madrid din inda kuma aka tabbatar da cewa ‘yan wasan kwallon Kwando na kungiyar sun kamu da cutar.
‘Yan wasan kwallon kafa da na kwallon Kwando na kungiyar ta Real Madrid din dai suna amfani da kayayyaki guda a filin atisaye na Ciudad Real Madrid.
Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta bayyana cewa “Gwaje-gwaje sun nuna cewa, daya daga cikin ‘yan wasan na kungiyar kwallon kwando ya kamu da cutar Kurona ta COVID-19”
“Tun da faruwar hakan, an bukace mu da mu killace ‘yan wasan kwallon kwandon da ma na kwallon kafa masu wasa a rukuni na farko, duba da cewa dukkansu suna amfani da filin atisaye na Ciudad Real Madrid.
“Haka zalika, an yanke hukuncin rufe filin atisayen da kuma kebe ma’aikatan filin atisayen saboda gwaje-gwajen.”
Hukumar ta La Liga ta bi sawun takwararta ta Italiya wajen sauke wasanni bayan wani taro a ranar Alhamis da hukumar kula harkokin kwallon kafa ta Sifaniya da kuma kungiyar ‘yan wasa.
An yanke hukuncin cewa, za’a sauke wasannin manyan gasa guda biyu a kasar wanda za’a buga a kwanaki 14 masu zuwa haka kuma za’a haramta shigan ‘yan kallo filayen wasa.
Shima wasan da Marid din zata buga da Manchester City a gasar Zakarun Turai a ranar Talata, na cikin tsaka mai wuya a dalilin lamarin.
Kungiyar Barcelona dai tuni ta sanar da cewa, baza a buga wasan da zata kece raini da Napoli a ranar Laraba tare da ‘yan kallo ba.
A wani bangaren kuma kungiyar UEFA na fuskantar matsin lambar sauke wasan baki daya.
Wasanni a Faransa, Jamus da kasar Portugal dai tuni aka fara yinsu ba tare da ‘yan kallo ba, yayin da kasar Italiya ta dage duk wasanni sai ranar 3 ga watan Afrilu.
Wata sanarwa da hukumar ta La Liga ta fitar ta ce “Duba ga yadda abubuwa suka kasance a safiyar yau na killace ‘yan wasan Real Madrid da aka yi da kuma gano cewa, wasu ‘yan wasansu sun kamu da cutar, hukumar La Liga sun damu da cewa, lamarin na iya yaduwa saboda haka ya dace ta dauki matakin dakile cutar Kurona ta COVID-19”
Sanarwar ta kara da cewa, “La Liga ta amince da sauke wasannin da za a buga makonni biyu masu zuwa.”
“Za a sake duba hukuncin da aka yanke bayan an killace kuma aka kammala gwaje-gwajen wadanda ake sa ran suna dauke da cutar.”
Alkaluman kididdiga dai sun nuna cewa, izuwa ranar Alhamis kasar Sifaniya ta tabbatar da mutum dubu 2,140 sun kamu da cutar yayin da mutum 48 suka rasa rayukansu.
Birnin Madrid yana daya daga cikin inda aka fi samun kamuwa da cutar a fadin kasar ta Sifaniya an ruwaito mutum 1,388 sun kamu kuma 38 sun rasa ransu.