Babban Limamin Masallacin Kasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari, ya caccaki Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) kan ci gaba da yajin aikin da take yi.
Malamin ya yi zargin cewa galibin malaman jami’a ba sa gudanar da cikakkun binciken da aka san malamai da yi, inda ya ce galibinsu kuma ba su cika shiga aji ya kai tsawon awa 10 sati ba.
- Ya kamata a gaggauta hukunta makasan Sheikh Aisami – JNI
- Zan iya tuka mota daga Abuja zuwa Kaduna babu ’yan rakiya – Ministan Buhari
Farfesan ya kuma ce akasarin malaman da zarar sun kai kololuwar mukamin Farfesa a jami’a sukan daina yin bincike, sakamakon ba sa bukatar wani karin girma.
Ya bayyana hakan ne a wani bidiyonsa da ya karade kafofin sada zumunta na zamani lokacin da yake tsokaci a kan yajin aikin malaman.
Farfesa Maqari dai tsohon malami ne a Sashen Koyar da Larabci na Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), kafin ya yi ritaya ya koma limanci ka’in da na’in a masallacin na Abuja.
Sai dai tuni kalaman nasa sun fara jawo ce-ce-ku-ce, inda tuni wasu daga cikin malaman jami’o’in suka fara mayar masa da martani.
Kimanin wata bakwai ke nan dai da kungiyar ta shiga yajin aiki kan zargin da ta yi wa Gwamnatin Tarayya na kin cika mata alkawuran yarjejeniyoyin da suka kulla da ita a baya.
Ga cikakken bidiyon bayanin nasa:
Prof. Sheikh Maqari fa ya jijjige teburin Yajin aikin ASUU baki daya… Allaah yasa mu dace. pic.twitter.com/3IDsaSdD1y
— ABU KHALID (@UsmanUaliyu35) August 24, 2022