✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farfesa Garba ya bukaci gwamnati ta taimaka wa malaman lissafi

Shugaba Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Ibrahim Garba, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta taimaka wa malaman lissafi a kowane mataki, domin bunkasa ilimin…

Shugaba Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Ibrahim Garba, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta taimaka wa malaman lissafi a kowane mataki, domin bunkasa ilimin lissafi a kasar nan.
Shugaban ya bayyana haka ne a wajen taron kara wa juna sani karo na 53 da kungiyar Malaman Koyar da Lissafi ta kasa ta shirya da aka gudanar a harabar jami’ar da ke Zariya.
Shugaban ya ce, koyar da ilimin lissafi na bukatar natsuwa da kayan aiki da kuma kwararrun malamai ta yadda dalibai za su fahimce shi sosai musamman da yake shi ne jigon ilimin kimiyya da fasaha, kuma yana taimaka wa a sauran fannonin ilimi.
A jawabin shugaban kungiyar ta kasa mai barin gado Muhammad Ibrahim, ya ce duk da cewa ana ganin lissafi fanni ne mai matukar wahala, amma matukar ana koyar da shi yadda ya kamata yana da sauki. Saboda haka ya yi kira ga masu ruwa-da-tsaki a kan harkar koyar da lissafi su bayar da gudunmawar da ta dace domin a samu nasara wajen koyonsa, “domin lissafi shi ne mataki na farko da duk mai koyon ilimin kimiyya da fasaha ya kamata ya sani,” inji shi.
Ya bayyana nasarorin da kungiyar ta samu musamman a lokacin shugabancinsa. Ya ce, kungiyar ta kammala ginin masaukin bakinta, kuma a halin yanzu shirye-shirye sun yi nisa wajen hada kungiya da hanyar fasahar sadarwa ta zamani.