Farfesa Nora Daduut ta Sashen Koyar da Harshen Faransanci na Jami’ar Jos ce, ta lashe zaben fid da takararar zaben cike gurbin kujerar dan Majalisar Dattawa mai wakilatar mazavar Filato ta kudu, a Jihar Filato karkashin inuwar jam’iyyar APC.
Farfesa Nora Daduut ta lashe zaben ne, bayan da ta kayar da wadanda suka fafata da ita a takarar.
- An daura auren Hanan diyar Shugaba Buhari
- Ba zan iya barin Barcelona ba, inji Messi
- Malamai 9,246 sun fadi jarabawar koyarwa
Za a gudanar da zaben cike gurbi na Sanata a mazabar ne, sakamakon rasuwar tsohon Sanatan da ke wakiltar ta, Sanata Ignatius LongJan a wata Fabarairun da ya gabata.
Da yake bayyana sakamakon zaben, Shugaban Kwamitin Shirya Zaven, Habu Isa Ajiya ya yi bayanin cewa Farfesa Nora Daduut ta lashe zaben ne da kuri’u 1,936.
Damian Shekarau ya samu kuri’u 61, Farfesa Doknan Shenni ya sami kuri’u 60 sai kuma Farfesa Emmanuel Garba wanda ya sami kuru’u 16.