Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaba daga inda muka tsaya a makon jiya:
Tasirin ’yan uwa da abokai
Wadansu ’yan uwan mata da na miji ko abokansu, masu jin haushin yakykyawar soyayyar da ke tsakanin ma’aurata, na iya hura wutar rikici a tsakaninsu, ta hanyar yada maganganun karya don ganin wannan soyayya ta samu nakasu.
Tasirin sinadaran rai
Soyayya lokacin samartaka tana da wani zaki da armashin da suka sha bamban da kowace irin soyayya. Masoya suna cikin tsananin so da kaunar juna, suna kewar juna, suna nuna kula ga juna, suna jin dadin kasancewa da juna, hatta murmushin da suke yi wa juna daban ne da kowane irin murmushin da sukan yi. A lokacin babban burinsu shi ne kasancewa tare har abada.
In Allah Ya kaddara suka auri juna, soyayyarsu lokacin amarci kuma ta fi ta lokacin samartaka, sukan ji kamar suna cikin wata aljannar duniya, wannan jin dadi har yakan bayyanu a siffarsu, inda annuri da annashuwa za su karu a fuskokinsu.
Amma a hankali sai soyayyar ta rika ja da baya, musamman da mace ta yi haihuwar fari, sai ya zamana zaman auren kawai ake yi. Maigida ya nemo abin kula da iyali ita kuma uwargida ta kula da gida da yara, amma wancan zakin soyayya na lokacin amarci da lokacin samartaka sun zama sai dai in ma’auratan sun tuna baya.
Sinadaran rai (hormones) na taka muhimmiyar rawa wajen kawo canje-canje a cikin soyayyar ma’aurata. Su ke zakaka dadin soyayyar samartaka da ta amarci, su ke rura wutar sha’awa a tsakanin masoya, domin aiwatar da babban aikinsu na tabbatar da yiwuwar saduwa tsakanin mace da namiji don macen ta samu ciki don jinsin dan Adam ya dore a bayan kasa.
Da an yi saduwar aure sai kaifin wadannan sinadarai ya fara raguwa, da macen ta haihu, to sun cimma burinsu, kuma sai su karkata wajen zuba tsananin soyayya da tausayin dan da aka haifa da son kula da shi sama da komai a zuciyar uwar. Sai ya kasance yanzu ba miji ne dan lele ba sabon jaririn nan shi ne dan lelenta.
Dabi’un maigida masu dakushe soyayya
1. Karin aure
Tsananin kishi da rashin so ko tsoron kishiya na sa so da kauna da yardar da ke cikin zuciyar uwargida game da maigidanta su rikide su koma kiyayya cikin kankanen lokaci.
Yawanci lokuta kuma doki da zakwadin da maza kan nuna ga uwargidan kafin da bayan karin aure da dabi’ar wulakanta uwargida da maishe ta ba komai ba da wadansu magidantan kan yi, duk suna cire soyayya da darajar maigida daga zuciyar uwargida, wanda daga baya ko da an an samu daidaitawa, sai ka tarar soyayyar ba kamar da ba, kafin faruwar haka, domin dai an ce ba a bari a kwashe daidai.
Rigakafin haka shi ne; duk maigidan da ke son samun dorewar kaunarsa da kimarsa da darajarsa a cikin zuciyar uwargidansa; to dole ne ya bi ta sannu-sannu ya kuma lallaba ta duk lokacin da ya tashi karin aure. Maigida ya san cewa wadansu matan kishi na sa su rasa kyakykyawan tunaninsu, su rika fadar maganganun da ba su dace ba, don haka sai a bi a hankali a dage da yin hakuri da wasu abubuwa da tsananin kishi ke kawowa. A kuma dage da nuna wa uwargida tsananin soyayya, duk wata ’yar karamar karyar da za ta kwantar mata da hankali ya halatta a yi mata, haka duk wani abu na kyautatawa da zai rage mata jin zafin kishi a daure a yi mata shi.
2. Tsananin takurawa
Wadansu mazan da zarar mace ta aure su, to shi ke nan kuma ta rasa ’yancinta, za su dabaibaye ta da tsauraran dokoki ta yadda komai dole sai abin da suke so za ta yi, hatta irin abinci ko dinkin kaya sai wanda suke so, ita ba ta da damar amfani da ra’ayin kanta da Allah Ya ba ta. Ko su rika yin kulle, ba zuwa makaranta, ba zuwa kasuwa ba sada zumunci da ’yan uwa; wani zai takura wa matar ta hanyar kin wadata ta da isasshen abinci da kayan masarufi alhalin yana cikin wadata. Wani ya hana neman ilimi alhalin tana tsananin son haka. Wani ya rika cutar da ita da bakaken maganganu na rainin hankali. Wani ya takura wa iyalansa da yawan fada, ko abu ya kai na fada, ko bai kai ba, ka ga uwargida gabanta na faduwa in ta ji sallamar maigida. To yaya kuwa zuciya za ta so abin da ke sa ta fargaba?
Maganin haka shi ne magidanta masu irin wannan hali su san wannan ba jarumta ba ce, domin wannan tsoro a hankali zai koma kiyayya mai tsanani, inda zai haifar da raini har ya kasance uwargida ba ta shakkar maigidanta. Annabi (SAW) Ya ce “Mafi alheri daga cikin maza shi ne mafi kyautatawa ga iyalinsa.” Don haka jarumin magidanci shi ne mai kyautatawa ga iyalansa ta kowace fuska.
3. Rashin kula da tsabtar jiki
In maigida ya kasance bai kula da tsabtar jikinsa da ta kayan sawarsa, a hankali zai daina burge uwargidansa, domin da ta kalle shi ta gan shi a hargitse, a yamutse, ba za ta so ci gaba da kallonsa ba. Kayatar da juna kuwa na daga cikin abubuwan da ke dumama soyayya a tsakanin ma’aurata. Ba yadda za a yi zuciya ta ci gaba da son abin da bai kayatar da ita ko yaya.
Maganin haka shi ne maza su sani, kamar yadda suke son ganin uwargida ta sha kwalliya musamman domin ta burge su, to, haka ita ma uwargida tana jin dadin ganin mijinta cikin kwalliya da shiga mai kyau. To amma in ka kusance ta kana wari, jiki ba gyara ba shiri, nan da nan za ta gundura da kai komai son da take maka.
Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.