Manoma a Jihar Taraba suna samun kudade masu yawa saboda tashin gwauron zabon farashin ridi da agushi da kuma shinkafa mai bawo a kasuwanni.
Wadannan kayan amfanin gona kwanan nan aka girbe su kuma manoma suka yi sa’a suka sami farashi mai kyau wanda aka dade ba a sami irinsa a jihar ba.
Binciken da Aminiya ta gudanar a kasuwannin hatsi da ke jihar ana sayar da buhu mai nauyin kilogram 100 na ridi a kan Naira dubu tamanin zuwa dubu tamanin da biyar.
Sai kuma buhun agushi wanda farashinsa ya kai Naira dubu hamsin zuwa dubu hamsin da biyar.
Ita kuma shinkafa mai bawo ana sayar da buhunta Naira dubu ashirin zuwa dubu Ashinrin da biyar.
Wani manomi mai suna Musa Muktari wanda dalibi ne a Jami’ar Maiduguri ya shaida wa wakilin Aminiya cewa ya yi amfani da lokacin yajin aikin malaman jami’a ya yi noman ridi kuma ya sami buhu 100.
Musa ya ce ya sami kusan kudi Naira miliyan tara bayan da ya sayar da ridin da ya noma.
Wani babban manomi mai suna Ali Maihula, ya ce bana manoman ridi da agushi sun sami kaka mai albarka ta yadda abin da suka girbe a gonakinsu ya zarce na shekarun baya kuma ga farashi mai kyau.
Ridi da agushi na da saukin nomawa kuma ba sa bukatar takin gida ko na zamani sa’annan sau biyu ake noma kowannensu a shekara.
Binciken Aminiya ya nuna cewa manoman da suka girbe ridi da agushi sun soma shirin sake shuka wannan kayan amfanin gona wanda za a girbe nan da karshen Nuwamba.