✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Farashin masara ya fadi warwas a Filato da Kaduna

Farashin ya karye a yayin da wadanda suka boye ta ke jira ta yi tashin gwauron zabo.

Farashin masara ya fadi warwas a wasu kasuwanni a sassan jihohin Filato da Kaduna.

Binciken da wakilinmu ya gudanar a babbar kasuwar hatsi ta garin Jingir, da ke Karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato, da babbar kasuwar hatsi ta yankin da yafi ko’ina noman masara a Najeriya wato garin Saminaka, da ke Jihar Kaduna, ya gano cewa farashin masarar, ya fadi ne saboda fara shigowar sabuwar masara.

Wakilin namu ya kuma gano cewa buhun tsohuwar masara da a baya ake sayarwa a wadannan kasuwanni a kan N21,000 zuwa N22,000 yanzu ya dawo N17,000 zuwa N18,000.

Buhun sabuwar masara da ba ta bushe sosai ba kuma ana sayarwa N13,000 zuwa N14,000.

Da yake zantawa da wakilinmu, kan wannan al’amari na faduwar farashin masarar, Sarkin Hatsin Kasuwar Hatsi ta garin Saminaka, Malam Manu Isah Idris, ya bayyana cewa lallai an samu faduwar farashin masara a kasuwar ta Saminaka.

Ya ce abin da ya kawo faduwar farashin masarar shi ne yanzu kamfanoni ba sa bukatar ta ga kuma shigowar sabuwar masara, shi ya sa farashin faduwa.

Shi ma da yake zantawa da wakilinmu, shugaban dillalan hatsi na kasuwar hatsi ta garin Jingir, Ishaku Alkali, ya bayyana cewa akwai wadanda suka ajiye masara da tunanin za ta kai N25,000 sai ga shi yanzu ta dawo N17,000.

Ya ce shigowar sabuwar masara da shigowar kayayyakin abinci, kamar doya da gwaza da dankali ne ya sa farashin marasa ya fadi a kasuwar.