Farashin mai da iskar gas sun ci gaba da tashin gwauron zabi a kasuwar duniya, inda a yanzu farashin ganga daya ta danyan man samfurin Brent ya kai dala 119, cirawa mafi girma cikin shekara 10.
A Turai ma farashin gas na ci gaba da tashi ba kakkautawa, kamar yadda farashin manyan kayayyaki irin su goran-ruwa wato aluminium, da kwal da alkama su ma ke kara tashi.
- Hanifa: Ba a cikin hayyacina na yi batutuwan da na yi a baya ba —Abdulmalik Tanko
- Jamus ta kwace jirgin ruwan wani attajiri dan kasar Rasha
Duk da cewa Amurka ba ta sanya cinikin mai da gas na Rasha cikin takunkumin da ta jagoranci sanya wa kasar ba a kan mamayar ta a Ukraine, zuwa yanzu ana dari-dari sosai a fannin ciniki da huldar kudade, wajen sayen kayayyakin Rasha.
Karin manyan kamfanonin duniya da kungiyoyi na takaitawa ko ma dakatar da harkokinsu a Rasha.
Kamfanoni na baya-bayan nan su ne IKEA, da Volswagen, da Spotify, da Citigroup, da H&M, da kuma uwa-uba Bankin Duniya.