Gwamnatin Tarayya za ta yi zama da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) bayan kungiyar ta yi barazanar fara zanga-zanga da yajin aiki kan karin farashin man fetur da wutar lantarki da aka yi.
Kakakin Ma’aikatar Kwadago ta Tarayya, Charles Akpan ya ce akwai yiwuwar Gwamnatin Tarayya za ta sanar da shirye-shiryenta na tallafi a lokacin zaman.
“Ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Dokta Chris Ngige za jagoranci zaman da za a yi da kungiyar kwadago.
“Taron zai gudana ne a ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2020 da misalin 3.00 na rana a dakin taro na Banquet da ke Fadar Shugaban Kasa”, inji shi.
- Zanga-zangar karin kudin mai da wuta na nan tafe —NLC
- NDLEA ta kama kwayoyi na miliyan N100 a zamfara
- Shin kun san abin da ya kawo tsadar kayan abinci?
A ranar Talata NLC ta ce za ta fara yajin aikin daga makon gobe muddin ba a janye karin farashin ba.
Da yake magana bayan taron kungiyar na kasa Shugaba NLC, Ayuba Wabba ya ce sun yi ittifakin tsunduma yajin aikin da zanga-zanga kuma babu lallashin da za su ji illa janye karin farashin.
A baya zaman da Gwamnatin Tarayya ta yi da kungiyoyin suka yi ya tashi ba tare da cimma matsaya ba kasancewar gwamantin ta ki janye karin farashin ko kuma bayar da tallafi ga ma’aikata domin rage radadin da karin ya haifar.
Daga bisani kuniyar NLC da takawararta ta TUC ta gammayar ma’aikata suka ce za su fara yajin aiki da zanga-zanga.