✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin kwandon tumatir ya kai N70,000

Yadda danyen tumatir ke gagarar magidanta da gidajen abinci a sassan Najeriya

Girki da danyen tumatir ya fara gagarar iyalai da gidajen abinci bayan farashinsa ya yi tashin gwauron zabo zuwa N70,000 a wasu jihohi.

Wakilanmu sun gano cewa a cikin ’yan makonni farashin babban kwandon danyen tumatir ya tashi daga kimanin N17,000 ya kai N70,000, musamman a Kudancin Najeriya.

A jihohin Kano da Katsina da Binuwai da ake noman tumatir, farashin babban kwando ya tashi daga tsakanin N17,000 zuwa N20,000 ya koma N40,000 zuwa 45,000.

A irin su Legas da Kwara da Oyo da Ribas da Enugu da Abuja kuma yana kaiwa Naira dubu 70.

Manoma na danganta tashin gwauron zabon danyen tumatir din da tsadar kayan noma da karancinsa da kuma annobar da ta lalata manyan gonakin tumatir.

A bangare guda kuma masu ruwa da tsaki na kira ga gwamnati da ta gudanar da bincike domin magance cutar tumatir da kuma samar da ingantaccen iri mai jure ruwa domin a samu wadatuwarsa a koyaushe a cikin kasa.

Farashin tumatir a jihohi

Aminiya ta gano cewa a halin da ake ciki farashin babban kwandon tumatir na kaiwa N40,000 zuwa N45,000 a Kano, sabanin Naira 15,000 da ake sayarwa a mako biyu da suka gabata.

A Fatakwal, Jihar Ribas, ya kai N65,000 zuwa N70,000, a Enugu kuma tsakanin N65,000 zuwa N68,000, ya danganci kasuwar.

A Jihar Legas, yana kaiwa N60,000 inda rahotanni suka nuna a Kasuwar Mile 12 ana sayar da babban kwando N62,000, sabanin farashinsa na N38,000 mako biyu da suka gabata.

A Jihar Binuwai farashin ya tashi daga tsakanin dubu 12 zuwa dubu 15 ya koma dubu 40 zuwa dubu 45.

Malam Isah Aliyu mai sayar da tumatir a Kasuwar Wadata da ke Makurdi, ya ce yana sayar da karamar roba N2,500, babban kwando kuma Naira dubu 40.

Wata mai gidan abinci a yankin Bwari da ke Yankin Babban Birnin Tarayya, Misis Azeez Kikilomo ta ce a kwanakin baya babban  kwandon danyen tumatir bai fi Naira dubu 18 ba, amma yanzu ya kai dubu 48 a Kasuwar Karmo.

A Jihar Kwara magidanta da gidajen sun ce farashin ya tashi daga Naira dubu 20 ya kai dubu 57 zuwa dubu 58.

Maman A’isha, mai sayar da kayan gwari a jihar ta ce “A wannan makon farashin ya haura zuwa tsakakin N45,000 zuwa dubu 65, gwargwadon irin kyansa.”

Idan dama ta ki…

Tashin gwauron zabon ya sa danyen tumatir ya gagari yawancin gidaje masu karamin karfi da gidajen abinci, inda suka koma amfani da na leda ko busasshensa.

Aminiya ta gano cewa Jihar Kano, daya daga cikin cibiyoyin noman tumatir a Arewacin Naira, ninkuwar farashin ya sa magidanta da dama komawa amfani da busashhensa ko na gwamnani.

Sai da sun bayyana cewa na gwangwanin da busasshen ba su kai danyen dadin dandano ba.

Wata matar aure kuma, Hajara Abdullahi ta koka da cewa a halin yanzu shi ma na gwangwanin ya kara tsada, “daga Naira 70 ya koma N120.”

Shugaban ‘yan kasuwar tumatir a Kasuwar ‘Yankaba da ke Kano, Mansur ‘Yankaba, ya ce annobar cutar tumatir mai suna Tuta,  wadda ta lalata manyan gonaki cikin ‘yan sa’o’i ce ta haddasa karancinsa a jihar.

“Yanzu yawancin wanda ake samu daga Bauchi da Maiduguri ake kawowa.”

Wani manomin tumatir a Jihar Kano, Jamilu Muhammad, ya ce dole a dauki mataki a kan cutar Tuta — wadda suka yi wa lakabi da Ebola — saboda cikin sa’a guda takan lalata gonar tumatir mai girman hekta biyar.

Ya ce, “Wata matsalar kuma ita ce rashin tumatir mai jure ruwa; sannan manoma na tsoro cewa damuna ta shigo, saboda haka ko mun shuka tumatir ba zai yi yadda muke so ba — sai dai mu yi asara.”

Da babu, gara babu dadi

Wata wadda ta je sayen tumatir a jihar Binuwai ta ce yanzu tumatirin leda shi ne mafita.

Misis Azeez Kikilomo mai gidan abinci a yankin Bwari da ke Yankin Babban Birnin Tarayya, ta shaida wa wakilinmu cewa dole ta sa ta koma yin girki da tumatirin gwangwani.

Magidanta da masu gidajen abinci a Jihar Kwara sun danganta tsadar danyen tumatir da tsadar kayan noma da cutar tumatir da aka yi fama da ita da kuma tsadar jigilarsa.

Don haka suka nema a kansu mafita ta hanyar amfani da na gwangwani ko busasshe ko kuma hakura da shi.

Wata matar aure, Lateefah Abdullahi ta ce, “Mun koma amfani da tumatirin gwamnani ko busasshen tumatir, duk da cewa bai kai danyen dadin dandano ba.

“Da busasshen tumatir ko na gwamngwani na Naira 200 zuwa 300 zan iya girki, amma idan danye ne, na Naira 500 ma sai dai in lallaba.”

Misis Azeez Kikilomo mai gidan abinci ta ce lamarin ya dagula mata lissafi domin komai tsadar tumatir dole sai ta yi amfani da shi.

“Ba mu da zabi, dole karin da aka samu ya kare kan kwastomomi; Mun kara farashin abinci, sannan mun rage yawan miyar da muke sawa,” in ji ta.

Matsalar karancin tumatir

Ita kuwa Maman A’isha wadda ta jima tana kasuwancin tumatir ta danganta tashin gwauron zabon da danyen ya yi da cutar tumatir da ta lalata gonaki a jihohin Kano da Jigawa.

“Duk lokacin da aka samu karancinsa daga Arewa tsada yake, duk da cewa muna komawa amfani da wanda ake samu daga yankin Kudu kamar daga Adooba da ke Ogbomso da kuma Asa, har zuwa watan Satumba, lokacin da za a fara samu da Arewa,” in ji ‘yar kasuwar.

Don haka suka yi kira ga gwamnati da ta yi mai yiwuwa wajen bullo da shirin da zai tabbatar da wadatuwarsa a kasa.

Ta bayyana cewa, “Yanzu maimakon manyan motoci 10 na tumatir da muka saba samu, bai wuci mu samu kananan bas ba; su ma din za ka sayar ne a kan yadda ka samu.

“Shekaru hudu da suka wuce, har Naria dubu 75 mun sayi tumatir saboda irin wannan matsalar.”

Shugaban Kungiyar Manoman Najeriya (AFAN) reshen Jihar Kwara, Umar Mahmud Aboki, ya alakanta tashin gwauron zabon tumatir din da tsadar rayuwa da ta shafi farashin kayan noma.

Ya ce, “Kafin yanzu mukan dauki ma’aikata a gonakinmu mu saya musu babur a kan Naira dubu 282, amma yanzu ya haura dubu 500.”

Wata mai suna Maria Akioye da kuma Isiaka Momoh sun alakanta tsadar da bukukuwan Karamar Sallah da aka yi a karshen watan Afrilu.

Maria da Isiya da suka je sayen tumatir a Jihar Binuwai, sun bayyana cewa an fi fama da karancin tumatir daga watan Mayu zuwa Oktoba, amam zuwa karshen shekara zai wadatu a jihar

Wani jami’in Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta Kasa da ya nemi a boye sunansa ya ce ma’aikatar na aiki tukuru domin dakile annobar Tuta da ke barnata tumatir.

Ya kara da cewa ma’aikatar tana kuma aiki domin inganta harkar noman rani ta yadda za a samu wadatuwar amfanin gona a kowane lokaci a fadin Najeriya.

 

Daga: Sagir Kano Saleh (Abuja) Hussein Yahaya (Kwara), Mumini Abdulkareem (Ilorin), Zahraddeen Y. Shuaibu (Kano) & Hope A. Emmanuel (Makurdi)