✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kudin kilon gas din girki ya kai N1,200

Dillalai na hasashen farashin kilo 12.5 zai kai N18,000 idan ba a dauki matakan da suka dace ba

’Yan Najeriya na kokawa kan tashin gwauron zabon gas din girki inda farashin kilo ke kaiwa N1,000 zuwa N1,200.

Wakilinmu a Kano ya ziyarci wasu cibiyoyin sayar da gas, inda ya lura farashinsa na N750 ya karu da akalla N250, inda yanzu yake N1,000, duk da cewa akwai masu sayarwa a kan 950, sai masu N880.

Tashin gwauron zabon gas din ya sa mutane kan yi tafiya mai nisa domin zuwa inda suke ganin za su samu da suke, ko da yake ba lallai hakarsu ta cimma ruwa ba.

Wata mata mai suna Suwaiba Ola da ta yi takanas daga Jihar Ogun zuwa Legas domin cika tukunyar gas dinta mai nauyin kilo 12.5 ta ce, “Tun daga Mowe na zo nan (Legas) na sayi kilo 12.5.

“N1,150 zuwa N1,200 ake sayar da duk kilo, saboda haka 12.5 zai iya haura N12,000, wanda ya yi tsada sosai, gaskiya da wuya idan zan iya ci gaba da kashe irin wadannan kudaden wajen sayen gas din girki.”

Da sake —’Yan Najeriya

A yayin da jama’a suke kokawa kan tsahin gwauron zabon gas din girki daga Naira 750, wasu iyalai sun fara hakura da shi sun koma amfani da gawayi da kuma ice wajen yin girki.

Wata matar aure Adebayo Esther Aderonke, ta ce “yanzu gas din girki sai wane da wane. A da sau uku muke dora sanwa a rana, amma yanzu za mu sake lale.”

Ita kuma wata mai gidan abinci, Chef Maya, ta ce tsadar gas ya sa: “mun kara kudin abinci kuma mutane na korafi, don haka muna fargabar rasa wasu daga cikin kwastomomin da muka saba da su.”

Dalilin tsadar

’Yan kasuwa sun dangata tsadar da tsadar kudin jigilar gas din a sakamakon tashin kudin bakin mai, a yayin da ’yan Najeriya ke zargin faduwar darajar Naira da karancin wurin ajiyar gas a sassan kasar.

Wani dalilin kuma, in ji shuganan dillalan gas din girki (LIPGAR) ta Jihar Kano, Muhammad Omede, shi ne “wahalar kawo gas din a sakamakon rashin kyan hanya daga Legas zuwa Kano.”

Amma wasu daga cikin ’yan kasuwa da wakilanmu suka tattauna da su a Legas sun ce suna fata gas din zai wadata a nan gaba.

A kwanakin baya jama’a sun yi ta rububin sayen gas din bayan da dillalansa suka sanar da shirinsu na kara kudi, ko da yake daga baya ya sauko, kafin yanzu ya sake tashi.

Kafin tashin gwauron zabon na gas a yanzu, sai da ya rika kamshin turaren dan goma a wasu sassan Jihar Kaduna, inda aka yi kwanaki ana farautar inda za a samu, saboda karancinsa.

Tsugune ba ta kare ba

Wani dillalin gas din a yankin Oshodi da ke Jihar Legas ya ce akwai yiwuwar kafin karshen makon da muke ciki farashin kilon gas zai koma N1,200.

Ya ce yanzu “N1,100 ne kilo daya, kilo uku N3,300, kilo 6 kuma N6,600 sannan kilo 12 a kan N13,200; yawanci idan mutane suka so sukan yi mamaki, wasu ma tafiya suke yi ba su saya ba.”

Shugaban kungiyar dillalan gas na kasa (NALGAM), Oladapo Olatunbosun, ya yi kira ga gwamnati ta dauki matakan hana tashin farashin, wanda ya auku a sakamakon karancin gas din a Legas.

A cewarsa, jirgin ruwan da ya kamata ya sauke gas a Legas har yanzu bai sauke ba, inda ya bayyana fargabar cewa idan ba a dauki mataki ba, farashin kilo 12.5 na iya kaiwa N18,000, idan har gwamnati ba ta dauki matakin da ya kamata ba.

A cewarsa, yanzu gas din da suke saya a kan Naira miliyan 8 ya koma Naira miliyan 14.5, don haka muddin da tsada suka saya, haka su ma za su sayar domi kudinsu ya fito.

“Gas din da jirgin ruwan ya kawo ba zai wadata ba, amma muna sa ran zai sake dawowa nan da mako guda, amma muna rokon gwamnati ta mayar da hankali kan bagnaren iskar gas, musamman ganin yadda cire tallafin man fetur ya kawo tsadar rayuwa, ga rashin isasshiyar wutar lantarki, mutane da yawa kuma sun dogara ne da gas wajen yin girki,” in ji shi.

Bai kamata gwamnati ta zura ido ba —Nasani

Wani kwararre a harkar mai da iskar gas Dr Dauda Garuba, ya ce tsadar gas za ta sa mutane da dama komawa yin girki da ice, duk kuwa da illar da hayaki yake wa muhalli.

“Makamashi abu ne da ya shafi tsaron kasa, saboda haka wajibi ne da ta dauki mataki, kar ta ce babu ruwanta da harkar kasuwnaci, 

“Idan saboda matsalar bangaren ne gwamnati ta tsame hannunta ta bar wa ’yan kasuwa, to shi shugabancin ba shi da matsala? Me ya sa ba ta cefanar da shi ba?”

 Gas zai wadata —Gwamnati

Wani jami’i a ma’aikatar man fetur ta kasa ya ce babu wani abin a zo a gani da gwamnati za ta yi kan tsadar gas din, tun da ta cefanar da bangaren.

Amma ya ce duk da hakka, gwamanti na kokarin ganin kamfanin iskar gas na kasa (NLNG) ya kara yawan wanda yake samarwa da nufin gani an samu saukin farashin.