✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mayakan ISIS da makamai Abuja

An kama mutum uku da ake zargin ’yan kungiyar ISIS ne tare da makamansu a yankin Birnin Tarayya

’Yan sanda na gudanar da bincike kan wasu mutum uku da ake zargin ’yan kungiyar ta’addanci ta ISIS ne da ka kama su dauke da makamai a yankin Babban Birnin Tarayya.

Jama’ar gari ne suka cafke na farko daga cikin mutanen dauke da bindiga kirar AK 47 a yankin Zuba, kafin ’yan sanda su kama sauran biyun tare da makamansu a yankin Dakwa.

Sarkin Padan Garin Zuba, Alhaji Murtala Muhammad ya shaida wa Aminiya a ranar Litinin cewa, an kama na farkon ne a kusa da tashar motar Dan-Kogo da ke Zuba ne a daren Lahadi dauke da bindiga kirar AK 47 da kuma kwansan harsasai guda biyu.

Sarkin Padan ya bayyana cewa, mutumina farkon da aka kaman ya iso garin ne a kan babur na haya, sannan ya nemi sake hawan wani.

“Sai dai bai kai ga hawan babur na biyun ba sai wasu matasa suka kula da bindiga da ya sakale ta cikin rigarsa, a nan ne suka tunkare shi, kuma suka samu nasarar kama shi,” inji Sarkin Pada.

Ya ce an garzaya da wanda a ke zargin zuwa fadan sarki kuma a yayin yi masa tambayoyi ya sanar da cewa shi dan kungiyar ISIS ne da ya zo Abuja da nufin kashe wani.

Sarkin Pada ya ce an sanar da ’yan sanda inda suka garzaya fadar suka wuce da shi babban ofishinsu na garin.

Ya ce daga bisani ’yan sandan sun sanar da shi cewa wanda aka kaman ya jagorance su zuwa maboyarsu da ke garin Dakwa a daren, inda aka samu nasarar kama wasu abokan harkarsa biyu tare da karin bindigogi kiran AK 47 guda biyu.

Da a ka tuntube ta, Jami’ar Hulda da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sanda ta Abuja, SP Josephine Adeh, ta yi alkawarin bin diddigin lamarin tare da yin karin bayani a kai, sai dai hakan bai samu ba har zuwa lokacin ai ka wannan rahotu.