✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin kayan abinci ya tashi —Ministar Kudi

Ta ce amma babu tabbas ko karin kudin mai zai kawo tsadar kayan abinci

Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmed ta ce farashin kayan abinci ya karu, sabanin abin da Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, wanda a makon jiya ya ce farashin kayan masarufi na raguwa.

Minista Zainab ta bayyana haka ne a hirar da gidan talbijin na NTA ya yi da ita a safiyar Litinin, inda ta ce tabbas farashin abinci ya karu, ko da yake ba lallai ne ya ci gaba da tashi ba.

“Gaskiya ne farashin abinci ya tashi kamar yadda na ce, tallafin da ya kamata shi ne wanda za bayar a bangaren samar da kayyaki ba a bangaren amfani da su ba”, inji ministar.

Sai dai ta ce da wuya farashin kayan su ci gaba da tashi ba saboda karin farashin mai, domin a cewarta yawancin mototin da ke dakon kayan abinci suna amfani ne da man dizel.

A makon jiya ne Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa, Garba Shehu ya ce farashin kayan abinci na raguwa.