Dubban mutane sun fito kan titunan kasar Faransa domin nuna adawa da shirin garambawul ga tsarin fansho da gwamnati ke niyar gudanarwa, lamarin da ya gurganta harkokin sufuri.
Harkokin sufuri sun gurgance a Paris babban birnin kasar, yayin da matatun man suka tsaya cak, su ma makarantu suka kasance a rufe sakamakon gangamin adawa da tsarin fansho.
- Fulani makiyaya na ficewa daga Taraba saboda yawan kai musu hare-hare
- Tsananin sanyi ya kashe mutum 70 da shanu 70,000 a Afghanistan
Dama dai kungiyoyin kwadago da dama sun yi kira ga ma’aikata da su shiga yajin aiki tare da halatar gangamin adawa da wannan mataki.
A fiye da garuruwa 200 na Faransa ne wannan gangamin ke gudana kamar yadda Gidan Rediyon Jamus DW ya ruwaito.
Ita dai gwamnati na son a kara shekarun yin ritaya daga shekaru 62 zuwa 64.
Bugu da kari kuma, adadin shekarun zubin kudin adashin gata don samun cikakken fansho zai karu sannu a hankali.
Wannan dai na zama babban kalubale a fannin siyasa ga Shugaba Emmanuel Macron a yanayi na matsin tattalin arziki, duk da danganta shi da yake yi da mataki mai muhimmanci a wa’adin mulkinsa na biyu.