Gwamnatin Faransa ta bayyana aniyar taimakon Najeriya wajen yaki da fashin teku a gabar ruwan kasar Guinea wanda aka dauki tsawon lokaci ana fama.
Hakan ya fito ne daga bakin Babban jami’in Tsaron Ofishin Jakadancin Faransa a Najeriya, Kanar Nicolas Rambaud, a ranar Laraba yayin ziyarsa a Cibiyar Horar da Sojin Ruwa ta Najeriya da ke Fatakwal.
- Jirgin yakin Birtaniya ya yi hatsari
- An yi jana’izar tsohon Limamin Masallacin Harami, Sheikh Al-Sabuni
- Fuskokin Limaman Sallar Tarawih da Tahajjud a Makkah
- Gobara ta babbake unguwar marasa galihu a Saliyo
Rambaud, ya ce “Muna sane da irin halin barazana da Najeriya ke fuskanta daga gabar ruwan Guinea.
“Za mu taimaki Najeriya wajen fito da sabbin tsare-tsare na horo ga sojin ruwa, don magance fashin jirage da garkuwa da mutane”.
Ya kara da cewa, Faransa na da muradai da dama wajen bunkasa alakarta da Najeriya, kuma wannan dama ce da za su nuna hakan a zahiri.
Jami’in ya ce sun gamsu da rawar da sojin ruwan Najeriya ke takawa kuma ta hanyar hadin kan da ke tsakanin kasashen, za a iya samun ci gaba.
Kanar Rambaud ya kuma yaba wa Najeriya saboda sayen jiragen yakin ruwa guda 17 daga kamfanonin Faransa a cikin shekarun da suka gabata.
Kazalika, ya sanar da cewa a cikin makonni masu zuwa Najeriya za ta karbi wani katafaren jirgin ruwan da ke dauke da na’urorin zamani daga Faransa.
Jirgin ruwan da ake wa lakabi da NNS Lana, yana dauke da ingantattun na’urorin zamani kuma zai bar Faransa ne a ranar 16 ga watan Afrilu zuwa Najeriya.
Kwamandan da ke kula da makarantar sojin ruwan Najeriya, Kaftin Mahmud Fana ya bayyana makarantar tasu a matsayin guda daya tilo a yankin Afirka ta Yamma.