Majalisar Dokokin Faransa ta amince da wani kuduri na biyan diyyar wadanda suka taya ta gwabza yakin neman ’yancin kai shekaru 60 da suka gabata.
Wannan ya biyo bayan matsayin shugaba Emmanuel Macron wanda a ranar 20 ga watan Satumbar 2021, ya nemi gafarar ’yan kasar Aljeriya da suka taimaka wa sojojin Faransa suka yaki masu fafutukar neman ’yancin kan kasar.
Sai dai an yi watsi da su bayan kasar ta sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 1962.
Bayan shafe shekara 60, yakin ya lakume rayukan mutum akalla 5000, wanda hakan ya sanya a baya-bayan nan Majalisar Dokokin Faransa ta mika kudurin.
’Yan majalisun dokoki kasar, akasarinsu daga bangaren masu ra’ayin rikau sun amince da hadin gwiwa a makon jiya dangane da bukatar sauya matsayin kasar a kan lamarin.
Sanata Marie-Pierre, ya ce sun kama hanyar sasantawa dangane da abin da ya faru a baya, yayin da Laurent Burgoa, ya ce babu wani lafazi da zai kauda radadin abin da ya faru.
Kudirin dokar ya ba da shawarar biyan diyyar tsakanin Yuro 2,000 zuwa 15,000 ga iyalan sojojin kusan 50,000 a kan kudi Yuro miliyan 310 a cikin shekaru 6.