✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Faransa ta kwashe ’yan kasarta da ’yan Birtaniya daga Libya

A shekaranjiya Laraba ne gwamnatin Faransa ta bayyana cewa ta kammala kwashe duka Faransawa da ’yan Birtaniya da ke zaune a kasar Libya sakamakon rikicin…

A shekaranjiya Laraba ne gwamnatin Faransa ta bayyana cewa ta kammala kwashe duka Faransawa da ’yan Birtaniya da ke zaune a kasar Libya sakamakon rikicin da ke faruwa tsakanin gwamnati da kungiyoyin da ke dauke da makamai a kasar.
Sanarwar ta ce Faransawa guda 40 ciki har da jakadan kasar da kuma ’yan Birtaniya bakwai ne  aka fitar da su daga Libyan ta jirgin ruwa. Har ila yau, ma’aikatar Harkokin Wajen Faransar ta bayyana rufe ofishin jakadancinta na birnin Tripoli.
kasar Libya ta tsunduma cikin rikici ne a shekarar 2011 bayan ratsawar guguwar sauyin da ta yi awon gaba wasu shugabannin kasashen Larabawa kasar.
A ranar Lahadin da ta gabata ne kuma kasar Amurka ta kwashe duka ma’aikatan ofishin jakadancinta da ke birnin Tripoli. Hakazalika, Majalisar dinkin Duniya itama ta bayyana kwashe ma’aikatanta da ke aiki a kasar.
Idan ba a manta ba, kasashen Faransa da Birtaniya ne suka taimaka wa ’yan tawayen kasar don hanbarar marigayi Shugaba Muammar Gaddafi daga mulki a shekarar 2011.
A ’yan kwanakin nan dimbin mutane ne suka rasa rayukansu sakamakon rikicin da ke faruwa a birnin Benghazi, garin da a ranar Laraba masu kaifin kishin Islama suka karbe iko da wani sansanin soji.